Kakakin IBB, Afegbua ya Magantu a Kan Haɗarin da Yake Fuskanta

 

A karon farko, mai magana da yawun Badamasi Babangida, Prince Kassim Afegbua, ya magantu a kan haɗarin da yake fuskanta.

Jigon na Jam’iyyar PDP bai bayyana ko ya kai kara ga ‘yan sanda ba.

Dan siyasar ya bayyana dalilin da ya sa yake fuskantar barazana daga wasu mutane da ba a san ko su wanene ba da kuma yadda ya magance lamarin.

Prince Kassim Afegbua, mai magana da yawun tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya bayyana cewa sau biyu yana tsallake rijiya da baya daga yunkurin kashe shi.

Tsohon kwamishinan yada labarai da wayar da kai na jahar Edo ya bayyana hakan a wata hira da jaridar The Nation wanda aka wallafa a ranar Asabar, 7 ga watan Agusta.

Kodayake Afegbua bai yi cikakken bayani game da yunƙurin da aka yi na kashe shi ba, amma ya bayyana cewa waɗancan yanayin sun kusa kai shi ga mutuwa.

Dan siyasar ya ce yana da tabo a duk jikinsa biyo bayan hare-haren. Afegbua ya bayyana cewa har yanzu yana samun barazana saboda ya kasance mai sukar gwamnati ne.

Ya ce:

“Har yanzu akwai barazanar saboda ina sukar gwamnati da rashin yin abin da ya dace. Ina tausayawa talaka. Na tsani ganin yadda mutane ke shan wahala saboda na san halin da na shiga kafin na kai wannan matsayin.”

Jigon na jam’iyyar PDP ya kuma bayyana Babangida a matsayin mutum mai hazaka, mai iya magana.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here