Sanata Orji Kalu ya yi Magana Kan Musulmi da Musulmi a Matsayin Shugaban Kasa da Mataimakinsa a Jam’iyyar APC

 

Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu ya tofa albarkacin bakinsa kan tsarin da APC ta ke so ta bi na tsayar da Musulmi da Musulmi a matsayin shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa.

Shugaban masu tsawatarwar a majalisar dattawa, ya ce kada kiristoci su ji tsoro koda anyi Musulmi da Musulmi domin matar Bola Tinubu Fasto ce.

Ya ce ko shakka babu uwargidar Tinubu wacce ke da ilimin siyasa za ta tsaya masu kasancewarta kirista kuma fasto.

Abuja – Shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Orji Uzor Kalu, ya tsoma baki a cece-kuce da ake ta yi kan batun tsayar da dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa daga addini guda.

Ana dai ta kai ruwa rana tun bayan da alamu suka nuna jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki na iya tsayar da Musulmi da Musulmi a matsayin yan takararta na kujerar shugabancin kasar.

Yayin da kungiyar kiristocin Najeriya ta yi watsi da shawarar sannan ta gargadi jam’iyyu a kan haka, wasu masu ruwa da tsaki sun bukaci yan Najeriya da su mayar da hankali kan cancanta fiye da akida.

Da yake jawabi ga manema labarai a majalisar dokokin tarayya a ranar Laraba, Orji Kalu ya bukaci kiristoci da su ji tsoro tunda matar Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyya mai mulki, Fasto ce, Daily Trust ta rahoto.

Jaridar Vanguard ta nakalto Kalu yana cewa:

“Bari na fada maku, a gidana, matata ce jagorar gida a zahirin gaskiya. Ko ku mazan da ke nan, yanzu da matanku basa nan, sune kan gida. Kamar idan na sanya wannan tufafin, matata za ta ce mun ‘mai gidana, wannan tufafin bai yi ba ka cire shi’. Matarka za ta fada maka Kosai da kunu ya kamata ka sha, ko za ka yi jayayya da ita, sai ka sha wannan kunun kuma matarka na so ka biya kudin makarantar yara, ko ka yi jayayya ko baka yi ba, sai ka biya kudin nan.

“Kiristoci su sanya ransu a inuwa saboda matar Tinubu Fasto ce kuma tunda fasto ce toh muna da kariya saboda ba matar gida bace. Tana da ilimin siyasa.”

Matar Tinubu, wacce a halin yanzu ke wakiltar Legas ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, an nada ta a matsayin mataimakiyar Fasto na Redeemed Christian Church of God (RCCG) a 2018.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here