An Kama ɗalibi  ya yi Shigar Mata Zai Zanawa  Budurwarsa Jarabawa a ƙasar Senegal

 

Dubun wani ɗalibin jami’a ta cika inda aka kama shi a ɗakin jarabawa yayi shigar mata a ƙasar Senegal.

Rahoto ya nuna cewa ɗalibin ya yi haka ne domin farantawa budurwarsa rai ya zauna mata jarabawa.

A halin yanzun an kama shi da budurwar tasa kuma an gurfanar da su a gaban mai shari’a.

Senegal:- Wani ɗalibin ƙasar Senagal ya shiga hannu bisa zargin ya yi shigar mata kuma ya zauna wa budurwarsa jarabawa, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Lauyan dalibin ne ya bayyana haka kuma yace ita ma budurwar tasa ta shiga hannun dukkan su a zarginsu da aikata zamba cikin aminci.

A halin yanzun saurayi da budurwar tasa an gurfanar da su a gaban kotu a kan karar aikata zamba da kuma haɗa kai don aikata zamba cikin aminci.

Channels ta ruwaito Lauya Serigne Ndiongue yana cewa:

“Gaba ɗaya waɗanda ake zargin suna fuskantar shari’a iri ɗaya domin sun aikata laifi da haɗin kan juna.”

A cewar mai gabatar da kara, Dalibin ya yi tafiya har zuwa tsakiyar birnin Diourbel domin ya rubutwa budurwarsa jarabawa a madadinta.

Hotuna sun watsu a kafafen sada zumunta Hotunan dake yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda ɗalibin ya saka kayan mata masu kalar ja da kuma abun wuya baƙi.

Rahotanni sun bayyana cewa mai kula da ɗakin jarabawa ne ya gano shi a rana ta uku bayan ya fahimci a kwai damuwa a yanayin shigarsa.

Daga nan kuma sai aka mika shi ga jami’an yan sanda domin su gudanar da bincike.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here