An Kama Masu Daukar Nauyin Boko Haram – Fadar Shugaban Kasa
Fadar shugaban kasa tace ta kama wasu wadanda ke da hannu a daukar nauyin ta’addancin Boko Haram.
Garba Shehu ya bayyana cewa za a fallasa bayanai a kan kamen da aka yi bayan kammala bincike kan lamarin.
Kamar yadda hadimin shugaban kasan ya sanar, ana zuwa har wuraren bauta domin halaka jami’an tsaro Gwamnatin tarayya ta ce jami’an tsaro sun damke wasu ‘yan Najeriya dake daukar nauyin ta’addancin Boko Haram.
Babban mai baiwa shugaban kasa shawara a harkar yada labarai, Garba Shehu, ya sanar da hakan a ranar Talata, 30 ga watan Maris yayin da ya bayyana a shirin siyasarmu a yau na gidan talabijin na Channels.
Read Also:
Legit.ng ta tattaro cewa, Shehu yace jama’a za su matukar girgiza idan suka ji bayanin binciken da ake kan makuden kudin da ake turawa kungiyar.
Ya ce wadanda aka kama sun hada da ‘yan canji dake zama a kasashen ketare. Shehu yace: “Yan canji ne ke turawa ‘yan ta’adda kudi.
Mun riga mun yi aiki da UAE. Mun damke ‘yan Najeriya dake turawa ‘yan ta’addan Boko Haram kudi kuma lamarin yana faruwa har a cikin gida.
Kuma ina sanar daku cewa idan mun gama bincike, sakamakon zai gigita ‘yan Najeriya.”
Ya kara da cewa, ‘yan ta’adda na kai farmaki wuraren bauta inda suke halaka jami’an tsaro, ya tabbatar da cewa jami’an bincike na sirri suna aiki a kan hakan.