Kotu ta Kama Google da Meta Kan Sakaci
Kotu a Amurka ta yanke hukuncin cewa kamfanin Meta da Google na da laifin sakaci, a wata gagarumar shar’ia da ta shafi jarabtuwa da amfani da shafukan sada zumunta.
Read Also:
Wata mata mai shekara 20 da haihuwa, mai suna Kaley, ce ta shigar da karar, inda ta alakanta matsalar tabin hankali da ta samu da yawaitar amfani da kafafen sada zumunta, tun tana ƙarama.
Kotun ta bayar umurnin a biya diyyar dala miliyan uku ga matar.
Ana dai ganin wannan shari’ar da aka yi a birnin Los Angeles, za ta yi tasiri ga sakamakon dubban shari’oi makamancin wannan, da aka shigar a kan kamfanonin fasaha, saboda gazawa wajen kare masu amfani da su daga jarabtuwa da amfani da dandalinsu.






