‘Yan Sanda Sun Kama Wadanda Suka Kashe Mahaifin Tsohon Gwamnan Plateau,Pa Defwan Dariye

 

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke wadanda suka kashe Pa Defwan Dariye, mahaifin tsohon gwamnan jahar Filato, Joshua Dariye, inji rahoton jaridar Punch.

An kashe dattijon dan shekara 93 bayan da masu garkuwa da mutanen suka sace shi suka kuma karbi kudin fansa miliyan 10 daga iyalansa.

Jagoran gungun masu garkuwa da mutane, Jethro Nguyen, dan shekara 53, ya ce ya dauki hayar wasu mutane 10 ciki har da wasu Fulani makiyaya don sace tsohon a gidansa, ya kara da cewa sun tsare shi a maboyarsu na kusan kwanaki 10 kafin su hallaka shi.

Nguyen, wanda aka gabatar da shi a hedkwatar rundunar sanda a Abuja, ranar Laraba 8 ga watan Satumba, ya furta cewa ya ba daya daga cikin ‘yan tawagarsa umarnin harbe tsohon.

Ya ce sun yi garkuwa da mamacin ne saboda za su iya samun kudi cikin sauki daga gareshi kasancewar dansa ya taba yin gwamna a jahar Filato, kuma sanata a Najeriya.

Karin bayani na nan tafe..

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here