An Kama Mutane 3 Bisa Zargin Kashe Mutane 18 a Afirka ta Kudu

 

Rundunar ƴansandan Afirka ta Kudu ta sanar da kama mutum uku bisa zarginsu da kashe wasu mutum 18 ƴanuwan juna a wani ƙauye bayan samamen da jami’anta suka kai.

Ministan ƴansandan ƙasar, Senzo Mchunu ne ya tabbatar da kamen a lokacin da ake addu’ar tunawa da mamatan 18 a ranar Lahadi a garin Lusikisikki da ke gabashin Cape inda aka yi kashe-kashen.

” Akwai mutum na huɗu da ake zargi da shi ma za su sanar da kama shi nan ba da jimawa ba”

An shiga damuwa ne a yankin bayan wasu ƴanbindiga sun buɗe wuta a wasu gidaje guda biyu, suka kashe mata 15 da maza uku, sannan ya jikkata wasu da dama.

Yawancin waɗanda harin ya shafa masu shekaru ne tsakanin 14 zuwa 64, kamar yadda jaridar Dispatch Live ta ruwaito.

Mchunu ya ƙara da cewa “har yanzu ƴansanda na ƙoƙarin gano musababbabin kisan”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here