SSS Sunyi Nasarar Kama Wasu Ma’aurata da Miyagun Makamai

Jami’an ‘yan sandan farin kaya sun kama wani Usman Shehu da matarsa, Aisha Abubakar da miyagun kaya.

Sun kama su ne a wani kauye da ke karamar hukumar Rimi a jihar Katsina, a ranar 22 ga watan Nuwamba.

Kakakin rundunar soji, John Enenche ya sanar da hakan a ranar Alhamis a wani taro na sojoji a Abuja.

Jami’an tsaro na farin kaya na jihar Katsina sun damki wani miji da matarsa da miyagun makamai.

Ana zargin Usman Shehu da matarsa Aisha Abubakar da ta’addanci. Kakakin rundunar soji, John Enenche, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taron da sojoji suka yi.

A cewarsa, an kama wadanda ake zargin a kauyen Abukur da carbi 14, caliber ammunition rounds 61 na 9.6mm da special ammunition rounds 399 na 7.62mm.

A cewarsa: “Rundunar soji sun kara samun wata nasara a ranar 22 ga Nuwamban 2020, inda ‘yan sanda masu fararen kaya na jihar Katsina suka damki wani Usman Shehu da matarsa Aisha Abubakar, a karamar hukumar Rimi da ke jihar Katsina.

“Jami’an tsaron sun yi kacibus da ‘yan ta’addan a daidai kauyen Abukur, suna dauke da miyagun makamai masu dumbin yawa. An kama su da magazines 14, rounds 61 na 9.6mm caliber ammunition da rounds 399 na 7.62mm special ammunition.”

VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here