Maganin ƙarfin Maza: NAFDAC ta Kama Mutane 24 a Sokoto
An kama masu sayar da magungunan karfin maza marasa rajista a jahar Sokoto.
NAFDAC ta ce kayan da aka kama a birnin Sokoto da kasuwa sun kai na Naira miliyan 2.
An gargadi mutane su guji shan magunguna marasa rajista da ake tallarsu cikin rana a titi da kasuwa.
Jahar Sokoto – Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna na kasa, NAFDAC, ta kama mutane 24 da ke talla da sayar da magungunan kara karfin maza na gargajiya mara rajista a garin Sokoto.
Shugaban hukumar na jahar Sokoto, Garba Adamu, ya bayyana cewa NAFDAC ta kama motocci shida da na’urar amsa kuwwa da ake amfani da su wurin sayar da jabun magunguna.
Ya ce kayan da darajarsu ya kai Naira miliyan 2 an kwato su ne a kasuwanni da titunan birnin Sokoto.
Read Also:
Ya ce za a tafi a yi wa magungunan da aka kwace gwaji sannan za a hukunta dukkan wadanda aka samu da hannu cikin lamarin don ya zama darasi ga wasu masu tallar.
Mista Adamu ya ce atisayen ya yi dai-dai ta umurnin da shugaban NAFDAC na kasa, Moji Adeyeye ta bayar na cewa tallar magungunan gargajiya a cikin rana ka iya janyo sauyawar sinadaren da ke cikinsu tare da kawo illa ga lafiyar mutane.
NAFDAC ta gargadi al’umma su guji shan magunguna marasa rajista
Ya yi kira ga al’umma su yi takatsantsan da magunguna marasa rajista, su kuma dena siyan kaya daga hannun masu tallar don taimkawa NAFDAC wurin tsare lafiyarsu.
A cewarsa, jami’an hukumar sun tsananta bincike a jahohin Kebbi da Sokoto ne domin tabbatar da ingancin kayayakin da ake sayarwa.
Ya kara da cewa za a cigaba da atisayen har sai an tsaftace harkar ya kuma yi kira ga masu magungunan gargajiya su rika bin dokokin gwamnati yayin gudanar da sana’arsu.
Mista Adamu ya jadadda cewa NAFDAC ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na tsare lafiyar ‘yan Nigeria.