Zabiya: Jami’an Tsaro Sun Kama Mahaifin da Zai Sayar da ‘Ya’Yansa

 

‘Yan-sanda sun kama wani mahaifi da ake zargi zai sayar da ‘ya’yansa zabiya guda uku a Mozambique.

An kama mutumin mai shekara 39 tare da kaninsa mai shekara 34, a lardin Tete da ke yammacin kasar a lokacin da ake cinikin.

Kakin ‘yan-sanda Feliciano da Câmara ya ce bayan su an kuma kama wasu mutane biyu da ake zargi za su sayi yaran.

Ana kashe zabiya domin amfani da sassan jikinsu wajen tsafi a kasar ta yankin kudancin Afirka.

Kakakin ya kara da cewa yaran uku masu shekara tsakanin 9 da 16, an dauke su ne daga gidansu aka tsare su a wani wuri yayin da cinikin ke gudana.

Cinikin ya haura sama da Dala 39,100 (ko Fam 32,400), in ji mai magana da yawun ‘yan-sandan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here