Jami’an Tsaro Na Farin Kaya Sun Kama Shugabannin CNG a Jahar Kaduna

Wasu da ake zargin jami’an tsaro na farin kaya (DSS) sun kama wasu shugabannin CNG a Kaduna.

Wadanda aka kama sune shugaban kungiyar, Ashir Shariff Nastura da kuma Balarabe Rufai, mai tsarawa na kasa.

Duk da dai ba a bayyana dalilin kama su ba, amma har yanzu an rasa hanyar da za a bi a gano inda suke, wayoyinsu basu shiga Wasu da ake zargin jami’an tsaro na farin kaya ne sun kama wasu shugabannin CNG a Kaduna.

Hakan ya faru ne bayan an dakatar da wani taro da kungiyar zata yi babu dadewa.

Wadanda aka kama sune shugaban BOT, Ashir Sheriff Nastura da kuma NC na kungiyar, Balarabe Rufai, The Nation ta wallafa. Kakakin kungiyar, Abdul-Azeez Suleiman ya sanar da manema labarai cewa har yanzu ba a san dalilin kama su ba don an kasa gano hanyar da za a bisu kuma wayoyinsu basu shiga.

Wasu da ake zargin jami’an tsaro na farin kaya ne sun kama wasu shugabannin CNG a Kaduna.Hakan ya faru ne bayan an dakatar da wani taro da kungiyar zata yi babu dadewa.

Wadanda aka kama sune shugaban BOT, Ashir Sheriff Nastura da kuma NC na kungiyar, Balarabe Rufai, The Nation ta wallafa. Kakakin kungiyar, Abdul-Azeez Suleiman ya sanar da manema labarai cewa har yanzu ba a san dalilin kama su ba don an kasa gano hanyar da za a bisu kuma wayoyinsu basu shiga.

Idan ba a manta ba, a ranar Laraba DSS ta kara jan kunnen mutanen da suke yunkurin kawo cikas ga zaman lafiyar kasa ta hanyar tayar da fadan addini ko na kabila a kasar nan.

Dama manyan kungiyoyin addini na Kasarnan kamar NSCIA, da CAN sun umarci DSS da ta daina zarginsu ta mayar da hankali ga masu tayar da tarzoma.

Duk da CNG bata sanar da jama’a ba, amma kungiyar ta shirya wani taro a ranar Laraba da daddare a NAF dake Kaduna amma ta mayar da taron zuwa ranar Alhamis 11:00am. CNG ta shirya taron ne don tasan yadda za ta bullo wa rikicin fatattakar Fulani daga kudancin Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here