An Kama Harsasai 7,500 da Tabar Wiwi ta N600m a Kebbi

 

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kebbi ta ce ta kama motoci biyu ɗauke da harsasai 7,500 da kuma tabar wiwi da darajarta ta kai ta naira miliyan 600.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandar a Kebbi, Nafi’u Abubakar ne ya bayyana hakan a yayin jawabin da yayi wa manema labarai a Birnin Kebbi, inda ya bayyana kamen da suka yi da cewa gagarumar nasara ce.

Ya ce ɗaya daga cikin motocin ta taso ne daga Ghana ta biyo ta Togo ta shiga Najeriya ta iyakar Jamhuriyar Benin, yayin da mota ta biyu ta taso daga Jamhuriyar Benin, kuma dukkanin su sun tsallake shigen jami’an tsaro da dama.

Ya ce “a ranar 10 ga watan Satum, da misalin ƙarfe 7:30 na yamma, tawagar jami’an ƴan sanda masu sintiri a yankin ƙaramar hukumar Bagudo sun kama babbar mota, ɗauke da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 4,927.”

Nafiu Abubakar ya ce ” babbar motar na ɗauke da harsasai 7,500 da kuma tabar wiwi da kuɗin ta za su kai naira miliyan 600″.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma ce ta kama mutum guda da take zargi da hannu kan wannan laifi.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com