A Kame Duk Malamin da Yake Wa’azin Tunzura Jama’a – Gwamna Zulum
Gwamnan jahar Borno, Babagana Umara Zulum ya bada umarnin kame malamai masu wa’azin tunzura jama’a.
Gwamnan ya bukaci hukumar DSS da su gaggauta cafke irin wadannan malamai masu ta da hankalin jama’a.
Ya kuma bukaci kungiyoyin addinai da su nemi izinin wa’azi daga gwamnatin jahar kafin gudanar da hakan.
Borno – Jaridar Punch ta rahoto cewa, gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya umarci jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da su kamo duk wani malamin da ke wa’azi a fili tare da tunzura jama’a kan junan su.
Read Also:
Gwamnan, ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da masu ruwa da tsaki a taron tattaunawa kan yanayin tsaro na jahar wanda ya samo asali daga mika wuya na daruruwan mayakan Boko Haram a gidan gwamnati ranar Lahadi a Maiduguri.
A cewar gwamnan:
“Wani muhimmin abu da nake son tattaunawa anan shine batun wa’azi a jahar. Idan ba a kula ba, wannan zai zama babban lamari saboda na ji masu wa’azi daban-daban sun fara cin zarafin juna.
“Na ji suna cin zarafin juna a wa’azin su. Na umarci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta kamo dukkaninsu a jahar.An bai wa Hukumar Hidimar Wa’azi dukkan ikon da za ta tsara ayyukansu.
“Ba za mu taba yarda wani ya shigo jahar ya fara fadin munanan kalamai ba, Kirista ne ko Musulmi.
“Wannan yana da matukar muhimmanci. Yakamata kungiyar CAN ta rubuta mana, Jama’atu Nasri Islam suma su rubutawa gwamnatin jahar Borno da hukumar hidimar wa’azi da nufin samar musu da damar yin wa’azi. Wannan yana da matukar mahimmanci.”