‘Yan Sandan Jahar Kano Sun Kama Mutane 7 Kan Kisan Fasto Yohanna

 

 

Rundunar yan sanda reshen jahar Kano, ta bayyana cewa ta damke mutum 7 da ake zargin suna da hannu a kisan wani malami a Kano.

Kakakin yan sandan jahar, Abdullahi Kiyawa, yace mutanen sun ce, suna zargin shugaban CAN da ɓoye wani mai laifi.

Rahoto ya nuna cewa Fasto Yohanna, ya jefa kanshi a cikin lamarin wani mutumi da mutane ke zargi da hallaka matar yayansa

Kano – Rundunar yan sanda ta tabbatar da kame mutun 7 dake da hannu a kisan shugaban ƙungiyar kiristoci (CAN) na ƙaramar hukumar Sumaila, jahar Kano, Shuaibu Yohana, kamar yadda Premium Times ta rawaito.

Mista Yohanna, babban malamin addinin kirista, ya rasa rayuwarsa ne a hannun wasu mutane kwanaki kaɗan da suka gabata.

Shugabannin ƙungiyar kiristoci na jahar Kano sun yi kira ga hukumomi da su tabbatar da adalci a kan ran ɗan uwansu.

Meyafaru da marigayi Fasto Yohanna?

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya fara ne ranar 22 ga watan Satumba, lokacin da wani Sabo Idris, ya kashe matar yayansa, bayan samun sabani.

Sai dai Fasto Yohanna, ya shiga cikin lamarin, inda mutane suka fara zarginsa da ɓoye Idris, wanda ya canza addini zuwa addinin kirista.

Bisa haka ne fusatattun mutanen yankin suka hallaka faston, kuma suka kone cocinsa, gida da kuma makarantar da yake jagoranta.

Wane mataki jami’an tsaro suka ɗauka?

Da yake fira da BBC Hausa ranar Litinin da yamma, kakakin yan sanda na jahar Kano, Abdullahi Kiyawa, yace jami’ai sun damke mutum 6 a wurin da aka aikata kisan.

Kiyawa yace:

“A binciken yan sanda, waɗanda ake zargin sun bayyana cewa sun zargi faston da ɓoye wani mutumi da ya kashe matar yayansa.”

“Daga baya wani mutum ɗaya ya kawo kansa, a halin yanzun mun kama mutum 7 dake da hannu a kisan faston.” “Wannan babban lamari ne da ba zai yuwu a kammala shi lokaci ɗaya ba. Muna bukatar hujja kuma yanzun muna kan hanyar bincike.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here