Da Zaran na Kammala Wa’adin Mulkina Zan bar Kaduna – El- Rufa’i

 

Gwamnan jahar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa da zaran ya gama wa’adin mulkinsa zai bar jahar Kaduna.

El-Rufai ya ce wannan ne dalilin da yasa gida daya kawai ya mallaka a jahar wanda ke a Unguwar Sarki.

Ya kuma bayyana cewar zai rage yawan ma’aikata a jahar musamman wadanda basu cancanta ba da kuma wasu da ya bai wa mukaman siyasa Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna ya bayyana cewa zai bar jahar da zaran ya kammala wa’adin mulkinsa.

El-Rufai, wanda ya shekara biyu yana wa’adin sa na biyu, ya fadi haka ne a wata hira da aka yi da shi ta kafafen yada labarai ta gidajen rediyo.

Ya ce ya mallaki gida daya ne kawai a yankin Unguwar Sarki da ke cikin garin Kaduna saboda a karshen wa’adinsa, zai bar jahar.

Ya ce ya mallaki gida daya ne kawai a yankin Unguwar Sarki da ke cikin garin Kaduna saboda a karshen wa’adinsa, zai bar jahar.

Gwamnan ya ce nan ba da dadewa ba gwamnatinsa za ta rage ma’aikata daga cikin tsarin biyan albashi na jahar.

Ya kuma kara da cewa baya ga ma’aikatan gwamnati zai kuma rage yawan wadanda ya nada a mukaman siyasa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“Bana satar kudaden gwamnati, bawai muna satar kudaden gwamnati bane don gina gidaje. Ina da gida ne a Unguwar Sarki kuma har zuwa yau shi ne gida daya tilo da na mallaka a Kaduna saboda bayan mulki na, ba zan zauna a Kaduna ba.

Don haka, ba zan kara wani gida a jahar ba,” inji shi.

“Gwamnatin jahar ba za ta biya albashin mutanen da ba sa aiki ba, saboda haka, lamarin zai shafi ma’aikatan da basu cancanta ba da wadanda ke sama da shekaru 50 ciki har da wadanda ma ba sa zuwa aiki a kai a kai kuma duk da haka ana biyansu albashi.”

Game da wadanda aka nada a mukaman siyasa, ya ce, “Muna duba yiwuwar rage nade-naden mukaman siyasa ne saboda idan ka rage wasu ka kasa rage naka, hakan zai zama rashin adalci. Tabbas za mu bincika mu rage wasu daga cikinmu a zahiri, tuni mun fara aiwatar da tsarin.”

Ya shawarci wadanda abin zai shafa da su je su nemi wani aikin, yana mai cewa an zabe shi ne don yi wa mutanen jahar aiki kuma zai yi iya bakin kokarinsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here