Jami’an Tsaro Sun Kamo Fursunoni 108 da ‘Yan Bindiga Suka Saki a Jahar Kogi

 

Jami’an tsaro a jahar Kogi sun yi nasarar kamo wasu daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan yari.

Idan baku manta ba, a jiya ne ‘yan bindiga suka farmaki gidan yari, suka saki wasu daga cikin fursunoni.

A halin yanzu ana ci gaba da bincike don kamo sauran wadanda suka tsere daga gidan na yari.

Kogi – Akalla fursunoni 99 daga cikin 294 da suka tsere daga cibiyar gyaran hali ta Kabba da ke jahar Kogi a ranar Litinin 13 ga watan Satumba ne jami’an tsaro suka kamo.

ThisDay ta ba da rahoton cewa a daren Litinin sama da sauran fursunoni 150 ne ba a san inda suke ba bayan da suka tsere. Jaridar da ta ambato wasu majiyoyi inda ta lura cewa wasu daga cikin fursunonin sun dawo bisa radin kansu.

An tattaro cewa wasu bayan sun fahimci mummunan aikin da suka aikata na tserewa sun mika kansu da kansu ga gidan na gyaran hali.

Haka kuma hukumar sa-ido ta jahar Kogi ta yi ikirarin cafke wasu fursunoni da ‘yan bindiga suka kubutar a cikin daji.

A cewar Haileru Dan Baba, kwanturola janar na hukumar gyaran hali, an fara gudanar da bincike kan lamarin don kamo wadanda suka tsere.

A rahoton da jaridar Punch ta fitar, wani jami’i a hukumar gyaran hali ya bayyana cewa, fursunoni 108 ne jami’an tsaro suka kamo tun bayan tserewarsu.

A cewar mai magana da yawun hukumar gyaran hali na Najeriya ga AFP ta wayar tarho:

“Muna da jimilar fursunoni 108 da aka kamo.” Ya kuma ba da tabbacin cewa, a hankali jami’an tsaro za su kara kamo sauran fursunonin da suka tsere.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here