Adadin Mutanen da Suka Kamu da Cutar Korona Ranar Sabuwar Shekara

Tun da aka samu ranar Litinin an dan samu sauki, adadin masu kamuwa da Korona ya karu.

A ranar karshen shekaran 2020, mutane 1031 ne suka kamu da cutar.

Har wa yau Najeriya bata sayo rigakafin Korona daga kasar Amurka da Ingila ba.

Mutane 1074 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Juma’a, 1 ga watan Junairu 2021, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Juma’a ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 88,587 a Najeriya.

Daga cikin kimanin mutane 90,000 da suka kamu, an sallami 74,373 yayinda 1294 suka rigamu gidan gaskiya.

Wani sabon nauyin cutar Korona da ya samo asali daga Ingila ya shigo Najeriya makonnin bayan nan.

Ga jerin jiha-jiha:

Lagos-642

Kaduna-92

Rivers-78

FCT-66

Gombe-66

Kano-35

Ogun-31

Katsina-22

Plateau-20

Abia-7

Niger-4

Oyo-4

Akwa Ibom-3

Delta-2

Osun-2

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here