Babu Lasisi: Jahar Kano ta Rufe Asibitoci Masu Zaman Kansu

 

Kano ta rufe wasu asibitoci masu zaman kansu guda uku wanɗanɗa aka gano suna aiki ba tare da rajista ba.

Asibtocin da ke karamar hukumar Kumbotso an rufe su ne a lokacin wani zagaye domin duba yada cibiyoyin lafiya ke gudanar da ayyukansu a Kano.

Sanarwar da Babban sakatare a hukumar gudanarwar asibitoci masu zaman kansu ya fitar, Dr Usman Tijjani Aliyu ya ce an gano asibitocin na ayyuka babu lasisi da bin dokoki da ka’idoji aiki.

A cewar sanarwar an rufe waɗannan asibitoci kuma za a dau matakan da suka dace da su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here