Hukumar Tace Fina-Finan Jahar Kano ta Dakatar da Nuna Fina-finai Dake Dauke da Shaye-Shaye, Kwacen Wayoyi da Garkuwa da Mutane
Hukumar tace fina-finan jahar Kano ta dakatar da nuna fina-finai dake dauke da ayyukan masha’a.
Hukumar ta hana nuna fina-finai dauke da garkuwa da mutane, shaye-shaye da kwatar wayoyi a jahar.
Sakataren hukumar, Ismaila Naaba Afakallah ya sanar da wannan umarnin wanda ya ce zai taimaka wurin hana ta’addanci.
Jahar Kano – Hukumar tace fina-finai ta jahar Kano ta hana nuna fina-finai da kuma sayar da fina-finan da suke dauke da garkuwa da mutane, shaye-shaye da kuma kwace wayoyi a fadin jahar kamar yadda LIB ta rawaito.
Read Also:
Sakataren hukumar, Ismaila Naaba Afakalla ne ya sanar da wannan umarnin inda ya ce anyi hakan ne don dakatar da yara daga koyon ta’addanci a jahar.
Hukumar ta dakatar da irin shirye-shiryen don taimakon tarbiyyar yara
Kamar yadda LIB ta rawaito, Afakalla ya ce:
“Daga yanzu, mun hana nuna fina-finai dake dauke da garkuwa da mutane, shaye-shaye da kuma kwacen wayoyi a fadin jahar.”
Afakallah ya bayyana cewa hakan zai taimaka wurin dakatar da hanyoyin da kananun yara za su yi koyi da ta’addanci.
Inda ya kara da cewa matsawar kananun yara sun ga jarumi yana aikata hakan za su iya koyi da shi.
Ya kara da cewa:
“Ba ko wanne karamin yaro ne zai iya gane cewa shirin fim bane. Yaro zai iya dauka da gaske lamarin yake faruwa don haka ya tafi ya aiwatar. Don haka wajibi ne a dakatar kafin ya auku.”