Jahar Kano Zata Mayar da Biyan Zakka Dole ga ‘Yan Siyasa – Safiyanu Abubakar
Daraktan hukumar Zakka ta jahar Kano, Safiyanu Abubakar, yace jahar na shirin mayar da Zakka dole ga masu damar biya.
Kamar yadda Abubakar ya sanar, daga yanzu duk wanda ke neman kujerar siyasa, sai ya nuna shaidar biyan Zakka.
Ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin rantsar da kwamitin Zakka a ofishinsa.
Darakta janar na hukumar Zakkah da Hisbah na jahar Kano, Safiyanu Abubakar, yace ana shirin mayar da biyan Zakka ya zama wajibi ga dukkan ‘yan siyasa kafin su tsaya takara a jahar.
Read Also:
Abubakar ya sanar da hakan a ranar Alhamis a ofishinsa yayin rantsar da kwamitin mutum 11 na karbar Zakka a jahar.
Kamar yadda yace, wannan al’amarin ana son tabbatar dashi ne domin taimakon mabukata a jahar.
“Ya zama dole ga kowannen mai hali ko kungiya da su fitar da wani kaso na dukiyarsu a matsayin Zakka,” yace.
Abubakar ya kara da yin bayanin cewa hukumar ta zo da wannan sabon salon ne ta yadda kowanne mai hannu da shuni zai biya zakka, “‘Yan majalisun jahar, ballantana na kwamitin lamurran addinin sun zauna tare da tattaunawa a kan muhimmancin Zakka.
“A matsayinmu na kwamitin, muna kokarin kaiwa matsaya ta yadda duk mai neman wata kujera a jahar sai ya bada shaidar yana biyan Zakka ga hukumar,” yace.