Jahar Kano ta fi ko Ina Zaman Lafiya a Najeriya – Gwamna Ganduje
Ganduje ya bayyana wasu irin matakan da gwamnatinsa ta dauka kan tsaro a Kano.
Ministan tsarin Najeriya, Salihi Magashi, ya ce Najeriya na cikin halin kakanikaye.
A cewar Ganduje, jahar Kano ta fi ko ina zaman lafiya a Najeriya Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Ganduje, a ranar Litinin ya bayyana cewa jahar Kano ta fi kowace jiha tsaro a Najeriya bisa matakan da gwamnatinsa ke dauka.
Ya yi alhinin matsalar rashin tsaro a Najeriya, musamman na karshen makon da ya gabata inda aka kaiwa gwamnan Benue, Samuel Ortom, hari. The Nation ta rahoton Ganduje ya yi wannan jawabi bayan ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Read Also:
Yace: “Abinda na sani shine a yau jahar Kano ce jaha mafi lumana a fadin tarayya kuma ba haka kawai bane, lallai akwai matakan tsaron da muke dauka, misali hadin kai tsakanin jami’an tsaro a Kano.”
“Mun samar da cibiyar leken asiri; CCTV inda muke kallon abinda ke faruwa cikin birnin Kano, mune masu na’urar bibiyan motoci mafi karfi a Kano.”
“A dajin Falgore inda yan bindiga ke zama, muka sam, ba zamu yarda a Kano ba. Mun kafa sansanin horon Soji a dajin saboda kada yan bindiga su zauna.”
Ganduje ya kara da cewa a Iyakar Kano da Kaduna, akwai daji a wajen kuma sun kafa wani shirin Ruga, sun tattauna da Fulanin daji, kuma sun amince zasu zauna wajen.
“Mun dauki dukkan wadannan matakai ne don samar da zaman lafiya a Kano,” Ganduje ya kara.