An Kama Mutumin da ya yi Karantsaye ga Tsaron Gidan Gwamnatin Jahar Borno

 

An kama wani Santiago Alexander da direbansa sakamakon yin karantsaye ga tsaron gidan gwamnatin jahar Borno.

Duk da dai jami’an tsaron gidan gwamnati sun dakatar da motar amma sam taki tsayawa ta nufi hanyar gidan Zulum gadan-gadan.

An nemi duk wata alama wacce za ta bayyana ko wanene shi amma sam babu a tare dashi, tuni ‘yan sanda suka damkesu.

Maiduguri, Borno – An kama wani Santiago Alexander, dan kasar waje wanda yace shi shugaban kungiya mai zaman kanta ne ta ACTED, bisa yin karantsaye ga dokar tsaro na gidan gwamnatin jahar Borno dake Maiduguri kamar yadda TheCable ta ruwaito.

TheCable ta gano yadda aka kama Santiago da misalin karfe 4pm a cikin wata mota mai kalar toka kirar Sienna mai lamba ta MAG 479 RM.

Santiago da direbansa sun nufi gidan Zulum kai tsaye.

Santiago, wanda ba a gane dan wacce kasa bane ya nufi gidan gwamna Babagana Zulum ba tare da wata alama da za a gane shi da ita ba aka dakatar dashi.

Direban Santiago mai suna Abubakar Suleiman bashi da wata alama da za a gane ko shi wanene a tare da shi.

Wanda ake zargin a cewarsa ya yi kokarin zuwa wani dakin taro ne na JPB da NC akan ayyukan cigaba amma kuma ya tafi gidan gwamnati.

Inda direban yace zasu je kusan nisan kilomita daya ne kuma ga alamu nan sarai da suke nuna cewa inda suka ce zasu je da bambamci da inda suka nufa.

Jami’an tsaro sun yi zargin akwai lauje a cikin nadi bayan an yi ta dakatar da motarsu amma suka yi kunnen uwar shegu dasu.

Sai da jami’an tsaro suka bisu da gudu kafin suka samu nasarar dakatar dasu.

An kara zarginsu bayan akwai alamu da dama na rubuce-rubuce da sauran hanyoyin da mutum zai gane inda suka ce zasu je da babu yanda za a yi a kasa gane wurin.

Santiago yace wani ya je gani a wurin taro.

Bayan an tambayi Santiago, wanda ba a gayyaceshi zuwa gidan gwamnati ba, ya ce an aike shi ya kai sakone zuwa wurin wani Oluseyi Fatuyi na bangaren hadin kan kasa da kasa dake karkashin ma’aikatar kudi dake a Maiduguri don yin taron JTB na kwana uku.

Fatuyi ya amsa cewa tabbas sun yi zasu hadu da Santiago.

Zulum ya umarci kwamishinan ‘yan sanda ya mayar da hankali wurin cigaba da bincike akan lamarin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here