Karin Bincike Game da Mutuwar Diego Maradona

 

Malaman asibiti sun yi bincike game da abin da ya kashe Diego Maradona.

Masanan sun tabbatar da cewa babu alamun Marigayin ya kwankwadi giya.

Matsalar koda da hanta da ciwon zuciya ne su ka taru su ka hallaka Dattijon.

An gano cewa tsohon tauraron Duniya, Diego Maradona ya rasu ne a sakamakon cututtukan hanta, koda da matsalar jijiyoyi da ya yi ta fama da su.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa binciken da aka yi ya nuna babu alamu ko burbushin giya ko wasu miyagun kwayoyi a jikin marigayin.

A ranar Laraba, 23 ga watan Disamba mai binciken ya bayyana abin da ya kashe tsohon ‘dan wasan. Mai binciken abin da ya hallaka ‘dan wasan a garin San Isidro, a birnin Buenos Aires ya wallafa sakamakon gwajin da aka yi a kan gawar marigayin.

An bukaci a gudanar da bincike a kan gawar Maradona ne domin tabbatar da cewa babu sakacin malaman asibitin da ke kula da shi a mutuwar ta sa.

Kafin tsohon kocin kwallon kasar Argetina, Maradona ya mutu, ya na fama da matsaloli da su ka hada da ciwon zuciya, ‘cirrhosis’ da matsalar koda.

Gwajin da masana su kayi ya nuna babu kwayoyi ko giya a jini ko bawalin Maradona, amma an tabbatar ya na shan magungunan kwantar da hankali.

An samu alamun magungunan cutar Ulcer da ciwon kai, da wahalar bayan-gida. Haka zalika an tabbatar cewa marigayin bai shan maganin ciwon zuciya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here