Ba za a Samu Bunƙasar Tattalin Arziƙi da ƙaruwar Arziƙi ba, Har Sai Mun Kakkaɓe Ta’addanci – Shugaba Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙara ɓullo da ƙwararan matakan tallafa wa Najeriya a yaƙin da take yi da ta’addanci, saboda mummunar iillarsa ga zaman lafiyar duniya da yadda yake tarwatsa mutane da ƙara haifar da fatara.
Ya yi wannan kira ne lokacin da yake jawabi yayin ganawa da ƙaramin sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya kan yaƙi da ta’addanci, Mista Vladimir Voronkov, a fadar gwamnati.
Shugaba Tinubu ya nunar da cewa ta’addanci ya yi ta mayar da hannun agogo baya ga harkokin ci gaban ƙasa da janyo ƙarin rashin kwanciyar hankali a tsakanin iyalai da al’ummomi, amma ayyukan haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Duniya wajen tunkararsa, sun kasance a tsittsinke kuma ana samun katsewar irin wannan tallafi ga ƙasashe masu tasowa.
“Jazaman ne daftarin Majalisar Ɗinkin Duniya, ya zama tushen duk wani ƙawance a nan gaba, maimakon bayar da tallafi”, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Juma’a.
Read Also:
“Mun yaba da duk abin da kuke yi. Mun san cewa duk da buƙatu da ƙalubalen da ke gabanku, za ku iya ƙarawa a kan ƙoƙarinku. Kun yi rawar gani a ayyukan haɗin gwiwar da kuke yi, amma ta fuskar tallafi a ƙasa, sai kun daɗa ƙoƙari. Sai kun ƙara jajircewa, saboda ta’addanci babban hatsari ne ga dimokraɗiyya, kuma hatsari ne ga ci gaban ƙasa.
“Ba za a samu bunƙasar tattalin arziƙi da ƙaruwar arziƙi ba, har sai mun kakkaɓe ta’addanci.
“Jazaman ne mu riƙa tunani a kan buƙatun jama’armu. A cikin ‘yar dukiyar da muke da ita yanzu, idan za mu riƙa kashe ɗumbin kuɗi, babu tallafi a kai a kai daga hukumomi kamar Majalisar Ɗinkin Duniya, to ba shakka muna cikin matsala,” shugaba Tinubu ya ce.
Da yake yaba wa gudunmawar Najeriya ga ƙoƙarin yaƙi da ta’addanci a duniya, ƙaramin sakataren na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya ce tuni Najeriya ta fitar da tsari a kan riga-kafi da dankwafewa da sulhuntawa, inda ya nanata yabo a kan ƙoƙarin da ƙasar ta yi zuwa yanzu don murƙushe ta’addanci.
Vladmir Voronkov ya kuma faɗa wa shugaban na Najeriya cewa Majalisar Ɗinkin Duniya na shirin gudanar da wani Taron Ƙoli kan Yaƙi da Ta’addanci a Abuja cikin watan Afrilun 2024.