Kashe Shugaban NECO: Rundunar ‘Yan Sanda da Jami’an NECO Sun Karyata Batun

Rundunar ‘yan sanda tare jami’an NECO sun bayyana gaskiyar abinda ya faru da shugaban NECO.

Sun ce lallai ba kashe shi aka yi ba, kawai ya mutu ne a cikin gidansa na Minna saboda karar kwana.

‘Yan sanda da hukumar NECO sun bayyana rahoton da ke cewa an kashe shugaban na NECO da zunzurutun karya.

A yau Talata ne aka wayi gari da labarin mutuwar shugaban hukumar jarrabawa ta NECO, wanda aka ce wasu ne suka kashe shi, jaridar Punch ta ruwaito.

Sai dai, majiyoyi masu karfi daga garin Minna a jahar Neja sun yi watsi da rahotannin da ke cewa an kashe Farfesa Godswill Obioma, shugaban na Hukumar Kula da Jarabawa ta Kasa (NECO).

A wata sanarwa da Legit.ng Hausa ta samo daga hukumar, NECO tace Obioma ya mutu ne kawai sabanin yadda aka ce wai an kashe shi.

A cewar wasu manyan jami’an NECO wadanda suka zanta da wakilin PM News, Obioma ya zo ne daga Abuja a safiyar Litinin, ba daren Litinin ba.

Jami’an NECO wadanda suka ziyarce shi da misalin karfe 9 na safe a gidansa da ke Dutsen Kura a Minna, Obioma ya fada musu cewa nan ba da dadewa ba zai fito zuwa ofishin na NECO.

Amma har zuwa karfe 2 na rana, Obioma bai bayyana ba, inda suka sake yin wata tawaga zuwa gidansa. Wakilan sun same shi shi kadai a cikin babban dakin kwanansa, yana kwance, yana fuskantar kasa matacce, lamarin da yasa aka kira dan’uwansa, wanda yake zaune a Minna akan yazo ya ga gawar.

Daga nan aka kwashi gawarsa zuwa Abuja. Rundunar ‘yan sanda da jami’an NECO sun bayyana labarin kisan a matsayin labarin karya da kuma shaidar matarsa, Elizabeth.

An nada Obioma, mai shekara 67, a bara a watan Mayu a matsayin shugaban NECO, kuma asalinsa ya fito ne daga jahar Abia.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here