ƙasashe 10 da Suka fi Biyan Mafi ƙarancin Albashin a Nahiyar Afirka

 

Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da ke biyan mafi ƙasa na karancin albashin ma’aikata a nahiyar.

Mafi ƙarancin albashin Najeriya a yanzu N30,000 ne, wanda ya ke daidai da kusan dalar Amurka 64.7 idan aka canza shi zuwa farashin CBN.

A kwanakin baya ne Najeriya ta cire tallafin man fetur, lamarin da ya sa ma’aikata a Najeriya suka buƙaci a kara musu mafi karancin albashin.

Biyo bayan cire tallafin man fetur da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi, ma’aikata a Najeriya sun fara tado da batun ƙarin mafi ƙarancin albashin da ake ba su a yanzu. Manazarta na ganin cewa Najeriya ce kusan ta ƙasa a biyan mafi ƙarancin albashin ma’aikata a nahiyar Afirka, duk kuwa da cewa ita ce ƙasa mafi karfin tattalin arziƙi a nahiyar.

N30,000 ba ta isar ma’aikatan wajen kwaranniyoyinsu A Najeriya, an ƙayyade mafi ƙarancin albashin a dalar Amurka 64.7, kimanin N30,000 a farashin canjin dala na N463 da babban bankin Najeriya (CBN) ya ƙayyade.

Babbar fargabar ma’aikatan dai ita ce, yadda mafi ƙarancin albashin da gwamnatin Najeriya ke biya a halin yanzu da kyar yake iya biya musu buƙatunsu.

Ma’aikatan sun ƙara shiga fargaba, biyo bayan cire tallafin man fetur da ya yi sanadin tashin farashin man da kuma tashin gwauron zabi na kayayyakin masarufi, harkokin sufuri da sauransu.

Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci gwamnati ta karawa ma’aikata albashi

Akan haka ne ma ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya suka yi barazanar shiga yajin aiki a duk faɗin ƙasar sakamakon ƙarin farashin man fetur ɗin.

Ƙungiyoyin ƙwadagon sun buƙaci gwamnati ta ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikata, wanda a halin yanzu yake a N30,000.

A cewar Nairametrics, ƙungiyar kwadago ta ƙasa (TUC), ta bayyana buƙatunta ga gwamnati bayan janye yajin aikin da ta shirya yi a fadin kasar sakamakon cire tallafin man fetur.

Ma’aikata sun bayyana bukatarsu

A wata sanarwa dake ɗauke da sa hannun shugaban kungiyar, Festus Osifo, da babban sakataren kungiyar, Mista Nuhu Toro, a ranar Litinin, 5 ga watan Yuni, 2023, TUC ta gabatar da jerin buƙatunta ga Gwamnatin Tarayya.

Buƙatun sun haɗa da a ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa N200,000 daga N30,000 da ake biya a yanzu kafin karshen watan Yunin 2023.

Haka nan kuma sun buƙaci gwamnati ta ɗage karɓar haraji daga ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu da ke samun ƙasa da N200,000 ko $500.

Albashin ma’aikata a kasashen waje Rahotanni sun bayyana cewa ƙasashe irin su Libya da ke fama da rikici, Seychelles, da wasu sauran ƙananun ƙasashen Afirka masu ƙaramin ƙarfi na biyan mafi karancin albashi ninki huɗu fiye da na Najeriya.

A koda yaushe, gwamnatin Najeriyar na bayar da uzurin cewa tana fama da ƙarancin kuɗaɗen shiga, shi yasa take gaza bayar da albashi mai ɗan gwaɓi ga ma’aikatan ƙasar.

Ga jerin sunayen ƙasashe 10 da suka fi biyan mafi ƙarancin albashin a nahiyar Afirka:

1. Seychelles: N200,000

2. Libya: N149,000

3. Maroko: N130,000

4. Gabon: N118,000

5. Afirka ta Kudu: N112,000

6. Mauritius: N111,120

7. Equatorial Guinea: N92,000

8. Kongo: N71,000

9. Algeriya: N70,000

10. Kenya: N65,000

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here