Sabon Hari: An Kashe ‘Yan Arewa 3 a Jahar Imo

 

‘Yan Arewa sun fara kaura daga jahar Imo sakamakon harin da ake kai musu.

An kashe yan Arewa akalla 11 cikin makonni biyu da suka gabata yanzu.

jahar Imo na fuskantar hare-hare kan yan sanda, fursunoni da yan kasuwa Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa an sake kai hari kan yan Arewa mazauna jahar Imo inda aka hallaka akalla mutum bakwai.

A cewar rahoton, wannan sabon harin ya auku ne makon da ya gabata inda aka kashe mutum hudu a Orlu kuma mutum uku a garin Amaka. Wani mazaunin Owerri, Dr. Lawan Yusuf, ya bayyana cewa yan kungiyar rajin kafa kasar Biyafara IPOB ne suka kai harin.

“Ko jiya yan IPOB sun kaiwa wasu ‘yan Arewa mahauta hari kuma sun kashe mutum uku. Mun ji jana’izarsu,” yace.

“Duk lokacin da suka hadu da yan Arewa a wurare kasuwancinsu, su kan tambayesu shine an basu izinin zama a kasar Biyafara, idan suka ce a’a, sai su lallasa mutum da makamansu; an kashe mutanenmu da dama ta haka.”

Yusuf ya ce an tura jami’an tsaro wuraren da yan Arewa suka fi yawa ne “amma babu jami’an tsaro a wasu wuraren kuma cikin tsoro muke rayuwa.”

Cikin makonni biyu da suka gabata yanzu, an hallaka akalla yan Arewa 11 a jahar Imo.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here