Katse Layukan Waya: Gwamnatin Kaduna ta musanta Jita-Jitar

 

Gwamnatin jahar Kaduna ta musanta wata jita-jita da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke cewa gwamnatin jahar na shirin katse sadarwa a jahar don yaki da ‘yan bindiga kamar yadda aka yi a jahar Zamfara.

Wata sanarwar mai ba wa gwamnan jahar shawara kan harkokin watsa labarai Muyiwa Adekeye, gwamnatin ta bayyana cewa bata tuntubi kowacce hukuma ta gwamnatin ƙasar da zummar neman a katse layuna sadarwa ba, don haka jama’a su yi watsi da batun.

“Zance ne mara tushe ballantana makama, babu wannan batu a jahar Kaduna, a bayyana muke komai da ya shafi tsaro, idan akwai wannan bukata za mu dauki matakin da ya dace.

Jahar Kaduna dai na cikin jahohin da suka fi fama da matsalar tsaro a Najeriya, kuma yayin da gwamnatin Zamfara ta katse layukan sadarwa, ana ganin suma sauran jahohin da ke maƙotaka da ita da ke fama da wannan matsala za su dauki irin wannan mataki nan gaba wataƙila

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here