Yadda Zan Kawo Karshe ‘Yan Bindiga a Jahar Zamfara – Sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Jahar
Sabon kwamishinan ‘yan sandan jahar Zamfara, Yakubu Elkana, ya ja kunnen ‘yan bindiga.
CP Elkana ya ce ko dai su zubar da makamansu ko kuma su yabawa aya zakinta a jahar.
Ya yi wannan furucin ne a Gusau ranar Laraba, yayin tattaunawa da manema labarai.
Zamfara – Sabon kwamishinan jahar Zamfara, Yakubu Elkana, ya ja kunnen shu’uman ‘yan bindigan da suka addabi jahar Zamfara inda yace ko dai su zubar da makamansu ko kuma su fuskanci hukunci mai muni.
Kamar yadda Channels TV ta wallafa, Elkana ya yi wannan furucin ne yayin tattaunawa da manema labarai a Gusau ranar Laraba, inda ya hori ‘yan bindiga suyi gaggawar baiwa gwamnatin jahar hadin kai wurin samar da zaman lafiya ko kuma su ga aiki da cikawa.
Abinda sabon kwamishina ya sanar da ‘yan bindiga.
sarin aikina cikin dabara zai fara, zamu yi amfani da salo na musamman wurin bi daki-daki don kawo karshen rashin tsaro a fadin jahar nan.
Zamu zabura wurin mayar da hankali akan yaki da duk wasu ‘yan ta’adda da masu taimaka musu sun fuskanci hukunci daidai da laifinsu ta hanyar amfani da jama’an gari wurin cimma wannan kudiri namu.
Read Also:
Jajircewarmu da mayar da hankalinmu a matsayin jami’an ‘yan sanda zai taimaka mana wurin gaggawar kawo karshen ta’addanci a jahar nan, sannan zamu yi amfani da tsare-tsaren da sifeta janar na ‘yan sanda ya samar da kuma hanyar samar da zaman lafiya da gwamna Bello Matawalle ya kirkiro.
Wannan shine abinda na mayar da duk hankalina akai a matsayina na kwamishinan ‘yan sandar jaharnan,” a cewar Elkana.
Yakubu Elkana ya roki jama’ar jahar alfarma.
Sannan kwamishinan ya kara da rokon jama’an gari da su yi kokarin baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro hadin kai wurin dakatar da duk wasu ta’addanci a fadin jahar.
A karkashin mulkina, ‘yan sanda zasu yi kokarin ganin sun yi amfani da kwarewa irin tamu don shawo kan kowacce irin matsala.
Zamu bi wasu hanyoyin don dakatar da ta’addanci, shiga hakkin bil’adama, rashawa da sauran miyagun ayyuka a fadin jaharnan,” a cewarsa.
Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, kwamishinan ya yabawa ‘yan jarida akan yadda suke baiwa ‘ya nsanda hadin kai don tabbatar da zaman lafiya a jahar.
Yan jarida suna kokari kwarai kuma mutanen kirki ne. Don yabon ku bata baki ne.
Don haka ina mika godiyata gareku akan hadin kan da kuke baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro,” a cewar Elkana.