Abinda ya Kawo Zancen Ministan Sadarwa a Zamun mu na Ranar Laraba – Femi Gbajabiamila

 

Majalisa ta ce ba a toshe korafin Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani ba.

Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya ce bai hana Ndudi Elumelu gabatar da kudirinsa ba.

Shugaban majalisar ya yi karin-haske game da abin da ya faru a zamansu na jiya.

Shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ya musanta cewa ya yi fatali da yunkurin kiran a sauke Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami.

Jaridar The Cable ta rahoto Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya na cewa bai dakatar da Honarabul Ndudi Elumelu lokacin da ya bijiro da maganar ba.

Da yake karin-haske a ranar Alhamis, Femi Gbajabiamila, ya ce abin da ya faru shi ne ya ci gyaran Tony Elumelu na kawo batun ba tare da bin ka’ida ba.

Shugaban majalisar wakilan yake cewa babu bukatar muhawara a game da irin wadannan batutuwa da kwamitin majalisa yake bincike a kansu.

Da aka yi zaman yau, ‘dan majalisar jahar Borno, Ahmed Jaha, ya ja hankalin majalisa da cewa ana zargin majalisa da toshe yunkurin a taba Ministan.

Honarabul Jaha ya ce: “A matsayina na ‘dan majalisar nan, abin da na fahimta shi ne majalisa ba ta hana shugaba marasa rinjaye kawo wannan batun ba.”

Jaha ya kare shugabansa, Gbajabiamila ya na cewa: “Shugaban majalisa ya fada wa (Elumelu) ya bi ta hanyar da ta dace. Babu wanda ya taka masa burki.”

Da yake yin martani, Femi Gbajabiamila ya yarda da abin da Jaha ya fada; “Kamar yadda ka yi bayani, Elumelu ya yi amfani ne da sashen doka ta shida.”

“Babu kudirin da aka kawo nan jiya.” Gbajabiamila ya bukaci ‘dan majalisar da ke da korafi a kan Ministan sadarwan, ya bi ta hanyar da doka ta bada dama.

Ana sa ran idan an koma zaman majalisa a mako mai zuwa, za a sake bijiro da maganar Ministan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here