Daƙile ‘Yan Ta’adda: Fani Kayode ya Yabawa Dr. Isah Pantami
Fani Kayode, ya yabawa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, bisa matakan da yake ɗauka a arewa.
Tsohon ministan jiragen sama ya kuma yabawa shugaba Buhari da kuma gwamnonin arewa maso yamma bisa kokarin da suke na magance yan ta’adda.
Kayode, sanannen mai sukar Pantami ne a baya, amma komai ya canza tun bayan haɗuwarsu a Kano.
Abuja – Tsohon ministan jiragen sama, Femi Fani Kayode (FFK), ya yabawa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Pantami, bisa “Saka yan ta’adda cikin halin tasku,” kamar yadda dailytrust ta rawaito.
A wani rubutu da ya yi, Kayode, ɗan adawan da ya koma abokim ministan sadarwa, ya kuma yaba wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Tsohon ministan ya yabawa manyan mutanen biyu ne ya yin da yake tofa albarkacin bakinsa kan matakin da aka ɗauka a arewa maso yamma don kawo karshen yan bindiga.
Shin matakan da ake ɗauka suna haifar da ɗa mai ido?
Tsohon ministan yace:
Read Also:
“A yan makonnin da suka shuɗe, an samu gagarumar nasara kan miyagun yan bindiga da yan ta’adda a yankin arewa maso yammacin Najeriya.”
“Jahar Zamfara ne lamarin ya fi ƙamari da kuma sauran jahohin yammacin arewa da suka haɗa da Katsina, Kaduna, Sokoto, Jigawa, Kebbi da kuma jahar Neja.”
“Abinda gwamnonin waɗan nan jahohin suka yi yana da ban sha’awa kuma ya sanya miliyoyin mutane cikin farin ciki a faɗin arewa da kuma ƙasa baki ɗaya.”
“Ina fatan gwamnonin kudu zasu jingine siyasa, su yi koyi da matakan da gwamnonin arewa suka ɗauka don kare rayuwar mutane.”
Wane matakai gwamnonin arewa suka ɗauka?
Kayode ya bayyana cewa ɗaya daga cikin matakan da aka ɗauka a Zamfara kuma ake shirin ɗauka a wasu jahohin arewa-yamma shine datse hanyoyin sadarwa.
Kayode yace:
“Wannan matakin ya daƙile yan ta’adda da kuma aikinsu na garkuwa da mutane kuma matakin ya baiwa kowa mamaki.”
“Maganar gaskiya minista Pantami ya yi namijin kokari wajen ɗaukar wannan tsattsauran mataki da haɗin kan gwamnan Zamfara.”
“Babu wani minista da ya dakushe yan ta’adda da ayyukansu cikin shekara 6 kamar Pantami kuma babu wanda ya kwatanta haka cikin gaggawa kamar shi.”