‘Yan Keke Napep na Jahar Neja Sun Shiga Yajin Aiki

 

Masu keke napep sun tsunduna yajin aikin gargaɗi a Minna, jahar Neja bisa matsin lambar da hukumomi ke musu.

Direbobin sun ce suna shan matsin lamba daga yan sanda, jami’an amsar haraji, jami’an VIO da sauransu.

Rahoto ya nuna cewa fasinjoji da dama sun tattaru yayin da masu yajin aikin suka toshe manyan hanyoyi.

Niger – Fasinjoji sun tattaru da safiyar Litinin a Minna, jahar Neja bayan direbobin napep sun shiga yajin aikin gargaɗi na yini ɗaya, kamar yadda dailytrust ta rawaito.

Fusatattun masu napep sun toshe hanyar Shiroro da shataletalen Mobil yayin da suke tilastawa duk wani ɗan nafef ya tsaya, sannan su sallami fasinjan da ya ɗakko.

Masu napep ɗin sun ɗauki wannan matakin ne domin nuna fushinsu kan yadda yan sanda, jami’an kare haɗurra, VIO, da masu karbar haraji suke matsa musu a yankin Chanchaga da Bosso.

Ɗaya daga cikin direbobin Napep yace:

“Banda matsin lamba da tsadar da jami’an amsar haraji suke mana a Chanchaga da Bosso kan dole sai mun rubuta lambar rijista a jikin keken mu da girma, wanda muke ganin zai lalata mana keke.”

“Yan sanda, jami’an hukumar kare haɗurra, da jami’an VIO suna matsa mana a kowace rana. Idan suka kama mutum suka tafi da shi ofishinsu dole sai ya biya N5,000 kafin su sake shi, abin ya yi yawa.”

Zamu cigaba da yajin aiki har sai an biya mana bukatun mu

Wani direban napep, Junaidu Abubakar, yace zasu cigaba da wannan yajin aikin matukar hukumomi suka gaza warware matsalolin su musamman abinda yan sanda da sauran hukumomin tsaro ke musu.

Ma ajiyin kungiyan masu nafef reshen jahar, Suleiman Danjuma, yace basu da masaniya, sun tashi da safe sun ga mambobin sun ɗauki wannan matakin.

Danjuma yace:

“Yajin aikin yana da alaƙa da yawan harajin da gwamnati ke karba, da yawan kame da jami’an VIO suke wa direbobin kan lamarin lambar rijista a karamar hukumar Chanchaga.”

“Ba wai suna adawa da rijistar bane amma yanda ake cewa su rubuta lambar a jikin keke yana bata musu abun sana’ar ta su.”

Fasinjojin Nafef sun shiga matsanancin hali

Wasu fasinjoji da suka zo daga wajen garin Minna ba tare da sanin abinda ke faruwa ba lamarin ya ritsa da su.

Wata mata, Aisha, wanda ta fito daga Paiko, ta shigo Minna domin siyan kayan abinci ta roki yan nafef da hukumomi su sasanta kansu domin talakawa su samu damar yin harkokin gaban su.

Duk wani kokari na jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan jahar, Wasiu Abiodun, ya ci tura.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here