Majalisar Dokokin Kenya ta Haramta wa Mambobinta Sanya Kayan Gargajiya

 

Majalisar dokokin Kenya ta haramta wa mambobinta sanya wata nau’in rigar kwat da ake kira Kaunda suit, wadda ta samo sunanta daga sunan tsohon shugaban ƙasar Zambia, marigayi Kenneth Kaunda.

Shugaban majalisar ya ce ba a maraba da kwat din da kuma wasu kaya na gargajiyar al’ummar Afirka a zauren majalisar, kasancewar sun ci karo da dokar sanya kaya ta majalisar.

Ya kuma jaddada aikin dokar a kan ƴan majalisa mata, wadda ta ƙunshi haramcin sanya gajerun siket da riguna bulawus marasa hannu.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com