Kirismeti: Adadin Mutanen da Suka Kamu da Cutar Korona a Ranar

 

Hukumar NCDC ta sanar da samun karin mutum 712 da suka kamu da annobar korona.

Wadanda suka kamu sun fito ne daga jihohi 20 na kasar.

A yanzu jimlar mutane 82747 ne suka harbu da cutar a kasar, yayin da 1,246 suka mutu, an kuma sallami 70,239.

Hukumar yaki da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC), ta bayyana cewa an samu karin mutane 712 da suka kamu da annobar korona a ranar Juma’a, 25 ga watan Disamba.

Hakan na kunshe ne a cikin sabbin alkaluman da hukumar ta wallafa a shafin Twitter. Ta kuma bayyana cewa karin mutane hudu sun mutu.

Sabbin mutanen da suka kamu sun fito ne daga jihohi 20 na kasar da suka hada da:

Legas: 388

Abuja: 77

Kwara: 39

Katsina: 35

Bauchi: 33

Plateau: 22

Ogun: 18

Akwa Ibom: 16

Delta: 13

Kaduna: 12

Osun: 12

Yobe: 11

Sokoto: 10

Kebbi: 8

Enugu: 6

Edo: 5

Ondo: 3

Niger: 2

Kano: 1

Oyo: 1

Gaba daya jimlar mutane 82747 ne suka harbu da cutar a Najeriya, yayin da 1,246 suka mutu sannan a yanzu an sallami mutane 70,239 bayan sun warke.B

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here