Dr Akunyili: Duk Wadanda Suke da Alhakin Kisan za su Fuskanci Hukunci a Duniya da Lahira – Shugaba Buhari

 

Shugaba Buhari ya tabbatar wa ‘yan uwan wadanda su ka rasa rayukansu su a harin da ya janyo kisan Dr Chike Akunyili cewa za a dauki mataki.

Kamar yadda shugaban kasar ya tabbatar mu su, duk wadanda suke da alhakin kisan za su fuskanci hukunci a duniya da lahira.

Shugaban kasar ya bayar da wannan tabbacin ne ta wata takarda wacce kakakin sa, Femi Adesina ya gabatar.

Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da ‘yan uwan wadanda su ka rasa rayukan su a farmakin da ya yi sanadin mutuwar Dr Chike Akunyili cewa, duk masu alhakin kai farmakin za su fuskanci hukunci a nan da lahira.

Shugaban kasan ya bayar da wannan tabbacin ne ta wata takarda ta ranar Laraba wacce kakakin sa, Femi Adesina ya saki, Daily Trust ta rawaito.

Kamar yadda Daily Trust ta wallafa, ya bukaci jami’an tsaro da shugabanni su hada kai wurin aiki tukuru don kawo karshen ta’addancin da ke cutar da ‘yan Najeriyan da ba su ji ba basu gani ba.

Buhari ya bayyana takaicin sa dangane da kisan gillar da aka yi wa Dr Chike, mijin tsohon darekta janar na hukumar kula da ingancin abinci da kwayoyi, NAFDAC, Farfesa Dora Akunyili.

A cewar Adesina, shugaban kasar ya bayyana radadin da yaran farfesan da Dr Akunyili da iyalan sa har da abokan arziki wadanda rayuwar su ba za ta taba kasancewa kamar da ba sakamakon zalunci da kisan rashin mutunci da ya auku a Onitsha da ke jahar Anambra.

“Shugaban kasa Buhari ya na tuna lokacin da yake aiki tare da Dora Akunyili a PTF kuma ‘yan Najeriya ba za su taba manta lokacin amazon ba, wanda ita kan ta Akunyili mace ce mai kwazo da kishin kasa,” kamar yadda takardar ta bayyana.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here