Bata Gari Sun Kona Gidan Jigon APC, Abubakar Usman

 

Benue – Rikicin jam’iyyar APC a Jihar Benue ya dauki sabon salo a yayin da wasu bata gari, a safiyar ranar Laraba suka cinna wuta a gidan jigon jam’iyyar APC, Alhaji Abubakar Usman wanda aka fi sani da Young Alhaji a Otukpo a Jihar Benue.

The Punch ta rahoto cewa wasu bata gari da ba a sani bane, misalin karfe uku na dare suka cinnawa gidan da ke GRA a Otukpo wuta.

Wutan ta cinye gaban gidan inda dakin mai gida da wasu gidaje suke.

Alhaji Abubakar, wanda ya taba yin sanata sai daya a Benue South, kwanaki kadan da suka wuce ya nuna akwatin gawa da littafin ta’aziyya don zolayar jam’iyyar APC a gaban gidansa.

Wasu yan jam’iyyar sun yi wa hakan fassara da cewa jam’iyyar APC ta mutu a jihar. Abubakar da wasu yan APC a jihar sun yi baje kolin akwatin gawar ne don nuna rashin jin dadinsu bisa zabin dan takarar mataimakin gwamna a jihar.

Abubakar ya tabbatar da afkuwar gobarar Da aka tuntube shi a wayar tarho, Alhaji Abubakar, wanda ya tabbatar da gobarar ya ce shi da kansa ya ajiye akwatin gawar a kofar gidansa don sanar da shugabannin jam’iyyar cewa akwai matsala a jam’iyyar a yankinsu.

Dakaci karin bayani …

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here