Dan Majalisar Wakilai Mai Wakiltar Mazaɓar Rogo/Karaye ya Bayyana Cewa Korarrun ‘Yan Bindiga Sun Fara Shigo wa Kano
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Rogo da Karaye, Haruna Isah Dederi, ya koka kan shigar yan bindiga jahar.
Kano A cewarsa yan bindigan dake gudowa daga luguden wutan rundunar sojoji a Zamfara da Katsina sun fara kai hari ƙaramar hukumar Rogo.
Majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin dakile yawon yan bindiga daga wani wuri zuwa wani.
Abuja – Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Rogo/Karaye ta jahar Kano, Haruna Isah Dederi, yace saboda luguden wutan sojoji kan yan bindiga a Zamfara da Katsina, sun fara tserowa suna shiga jahar Kano.
Read Also:
A wani kudiri da ya gabatar a zaman majalisa na ranar Talata, yace a yan makonnin da suka gabata mahara sun kai hari wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Rogo.
Dailytrust ta rahoto cewa ƙauyukan da hare-haren ya shafa sun haɗa da Jajaye, Zarewa, Ruwan Bago, Bari, Falgore, DutsenBan da Hawan -Gwamna (Fulatan).
Ya kamata a ɗauki matakin gaggawa – Dederi
A jawabinsa, ɗan majalisar yace:
“Idan ba’a ɗauki matakin gaggawa ba domin dakile ayyukan waɗannan yan bindigan a ƙaramar hukumar Rogo da sauran yakunan dake karshen iyakar Kano.”
“Maharan zasu watsu zuwa sauran yankuna, kuma haka barazana ne ga zaman lafiyan jahar.”
Wane mataki majalisa ta ɗauka?
Bayan sauraron wannan kudiri ne, majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ankare da abinda nasarar da sojoji ke samu a Zamfara da Katsina ke jawo wa.
Ta hanyar ɗaukar matakai a sauran jahohin da lamarin ya shafa domin dakatar da sauya gurin yan bindiga daga wannan wurin zuwa wani na daban.