Yaduwar Cutar Korona: Dokokin da Gwamnatin Tarayya ta Saka

 

Gwamnatin tarayya ta saka sabbin dokoki a sakamakon yadda cutar korona ke yaduwa.

PTF ta sanar da cewa gwamnatin tarayya ta bukaci rufe dukkan mashaya, gidajen rawa da wuraren nishadi.

Ana bukatar dukkan jihohi 36 tare da birnin tarayya su bi sabbin dokokin na tsawo makonni biyar.

Gwamnatin tarayya ta kakaba wasu sabbin dokoki yayin hauhawar yaduwar cutar korona a fadin kasar nan, Channels TV ta wallafa.

Boss Mustapha, wanda shine shugaban kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da korona, ya sanar da hakan a ranar Litinin bayan bayanin da yayi ga kwamitin a birnin Abuja.

Ya bayyana cewa wannan umarnin sun fito ne daga mashawarta inda aka mika su ga jihohi a kan a tabbatar da su na tsawo makonni biyar.

Sabbin ka’idojin sun hada da rufe dukkan mashaya, gidajen rawa da wuraren taro. Rufe dukkan wuraren nishadi a dukkan jihohin kasar nan da birnin tarayya.

An bukaci dukkan gidajen cin abinci da su rufe ban da wadanda ke samar wa mazauna otal, wadanda ba a ci a ciki da kuma masu kaiwa har gida.

Hakazalika, dukkan tarukan da suka hada da biki, siyasa, nishadi, motsa jiki, liyafar karshen shekara da sauransu duk kada su wuce mutum 50.

Gwamnatin ta takaita tarukan addinai da kada a wuce kashi 50 na wurin bautar sannan a kiyaye dokokin nesa-nesa da juna tare da saka takunkumin fuska.

Kamar yadda Mustapha ya ce, duk wani taro da za a wuce mutum 50, toh ya zama dole a yi shi a budadden wuri.

Ya kara da cewa duk wasu nau’in sufuri dole ne su dauka rabin yawan fasinjojin da suke dauka domin biyayya ga dokar nesa-nesa da juna.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here