Kotu ta Amince da Goodluck Jonathan ya yi Takarar Shugaban ƙasa

Babbar Kotun Tarayyar Najeriya da ke zama a Yenegoa babban birnin Bayelsa ta yanke hukuncin cewa tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai iya takarar shugabancin ƙasar

Jaridun Najeriya sun rawaito cewa alkali mai shari’a Isa Hamma Dashen ne ya yanke wannnan hukunci a ranar Juma’a.

Sai dai har zuwa yanzu Jonathan bai fitar da wata sanarwa ba da ke nuna cewa zai tsaya takara.

Ko a kwanakin baya sai da gamayyar kungiyoyi a arewacin Najeriya suka saya wa Jonathan tikitin takarar shugaban kasa karkashin Jam’iyyar APC, duk da cewa Jonathan ɗin ya nesantar da kansa daga tikitin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here