Kotun Zaɓe ta Tanadi Hukunci Kan ƙalubalantar Nasarar Gwamna Nwifuru
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Ebonyi ta tanadi hukuncinta kan ƙalubalantar nasarar ɗan takarar jam’iyyar APC, Francis Nwifuru.
Ƴan takarar PDP da APGA na ƙalubalantar cewa Nwifuru wanda ya lashe zaɓen, ba cikakken ɗan jam’iyyar APC ba ne a lokacin zaɓen.
A nasa martanin, lauyoyin ɗan takarar jam’iyyar APC sun bayyana cewa Nwifuru ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC kafin zaɓen fidda gwanin gwamna, sannan zaɓen shi bai saɓa wa ƙa’ida ba.
FCT, Abuja – Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Ebonyi mai zamanta a Abuja, ta tanadi hukuncinta kan ƙarar da ɗan takarar gwamnan jam’iyyar PDP, Ifeanyi Odili da na jam’iyyar APGA, Farfesa Benard Odoh, suka shigar.
Read Also:
Kotun ta tanadi hukuncin na ta ne bayan dukkanin ɓangarorin sun kammala miƙa bayanansu, cewar rahoton Channels TV.
Legit.ng ta tattaro cewa ƴan takarar na PDP da APGA na ƙalubalantar bayyana ɗan takarar APC, Francis Nwifuru a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan na ranar 18 ga watan Maris 2023.
Nwifuru ba ɗan APC ba ne, cewar masu ƙara
Masu shigar da ƙarar na son kotun ta soke nasarar Nwifuru kan dalilin cewa shi ba cikakken ɗan jam’iyyar APC ba ne a lokacin zaɓen.
Sun yi zargin cewa gwamnan jam’iyyarsa ba ta ɗauki nauyinsa yadda ya dace ba, inda suka ce har a lokacin zaɓen shi ɗan jam’iyyar PDP ne.
Sai dai, lauyan ɗan takarar na APC, Arthur Okafor, ya bayyana cewa wanda yake wakiltar cikakken ɗan jam’iyyar APC ne kuma ya lashe zaɓen ne a bisa ƙa’ida.
Ya bayyana cewa gwamna Nwifuru lokacin da yake shugaban majalisar dokokin jihar, ya fice daga PDP sannan ya koma APC kafin ya nemi takarar gwamna a jam’iyyar ta APC, rahoton Premium Times ya tabbatar.