Kotu ta Soke ‘Dan Takarar Kujerar Gwamnan APC a Jihar Taraba
Kotu ta fitittiki dan takarar kujerar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Taraba, Sanata Emmaneul Bwacha.
Kotun tarayya ta baiwa hukumar INEC umurnin ta gaggauta shirya sabon zaben fidda gwani.
Lauyoyin Bwacha sun bayyana cewa zasu daukaka kara ko kuma ayi sabon zaben kawai.
Jalingo – Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Jalingo, jihar Taraba ta soke zaben Emmanuel Bwacha a matsayin dan takaran gwamnan jihar na jam’iyyar All Progressives Congress APC.
Soke zaben Bwacha ya biyo karar da daya daga cikin yan takara, David Sabo Kente, ya shigar.
Read Also:
Kotun ta bayyana cewa bisa hujjojin da aka gabatar gabanta, ba’ayi zaben fidda gwani a Taraba ba, rahoton ChannelsTV.
Alkali mai shari’a, Simon Amodeba, ya bada umurnin yin sabon zabe cikin kwanaki 14.
Alkali ya umurci Hukumar zabe ta kasa INEC ta soke sunan Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar gwamnan jihar Taraba na jam’iyyar APC.
Alkali yace ba zai yiwu mutum daya ya rubuta dukkan sakamakon zaben ba yayinda baturen zaben yace babu zaben da ya gudana a jihar lokacin da aka tsareshi a hedkwatar yan sandan jihar saboda barazanar da ake yiwa rayuwarsa.
Lauyoyi APC da Bwacha sun bayyana cewa zasu karanta shari’a kafin daukaka kara ko kuma su shiga sabon zabe…