Kotu ta Soke Nasarar Dan Majalisar Jihar Enugu na Jam’iyyar LP

 

An soke nasarar zaben Honourable Bright Ngene na jam’iyyar Labour Party a jihar Enugu.

Kotun sauraron kararrakin zaben majalisar dokokin jiha ta tsige Ngene a ranar Laraba, 13 ga watan Satumba.

Saboda haka kotun ta yi umurnin sake sabon zabe a mazabar Enugu ta kudu cikin kwana 90.

Jihar Enugu – A ranar Laraba, 13 ga watan Satumba ne kotun sauraron kararrakin zaben majalisar dokokin jiha da ke zama a jihar Enugu, ta soke ayyana Honourable Bright Ngene na Labour Party a matsayin dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Enugu ta Kudu.

Da yake soke zaben, kwamitin mutum uku karkashin jagorancin A. M. Abubakar ya bayar da umarnin sake gudanar da sabon zabe a mazabar Enugu ta Kudu cikin kwanaki 90, kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto.

Dalilin da yasa kotu ta tsige dan majalisar Labour Party Ngene Da take fadin dalilin soke zaben, kotun zaben ta ce hakan ya kasance ne saboda adadin kuri’un da aka ce wanda ya lashe zaben ya samu bai kai adadin na wadanda aka hana yin zabe a mazabar ba.

Saboda haka, kotun ta ce hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta yi kuskure da ta ayyana Bright Ngene a matsayin wanda ya lashe zaben.

Ta kara da cewar da kamata ya yi ace hukumar zaben ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba sannan a sake sabon zabe a wuraren da ba a gudanar da zaben ba saboda tazarar da ke tsakanin manyan yan takarar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com