Kotu na Tuhumar Jami’an Tsaron Falasdinu 14 Kan Kisan Fitattacen Mai Fafutika, Nizar Banat

 

An gurfanar da wasu jami’an tsaron Falasdinu su 14 gaban kotu dangane da tuhumar da ake yi musu kan kisan wani fitattacen mai fafutika, Nizar Banat.

An karanta mu su tuhumar da ake yi mu su , sai dai dukkaninsu ba su amsa wannan laifi ba.

Rahotanni na cewa dukkannin wadanda ake zargin jami’ai ne masu rike da kananan mukamai a rudunar tsaro da ke yaki da miyagun laifuka kuma ana zargin suna cikin wadanda suka yi wa Nizar Banat duka.

An age shari’ar zuwa makon gobe.

Nizar Banta wanda ya rika sukar shugaban Falasdinu da mukaranbansa an yi masa duka kuma ya rasa ransa jim kadan bayan da aka kama shi a watan Yunin da ya gabata.

Mutuwarsa ta haifar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da mahukunta Falasdinu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here