Kotu ta Kara Bada Umarni Kama Abdulraseed Maina

Babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Abuja ta bukaci a kama Abdurasheed Maina a duk inda aka gan shi.

Sanata Ali Ndume, mai wakiltar jihar Borno ta kudu, ne ya karbi belin Maina a kan kudi miliyan N500.

Kafin Ndume ya karbi belinsa, Maina ya shafe watanni bakwai a gidan yarin Kuje da ke birnin tarayya, Abuja Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Abuja.

ta bayar da umarnin janye belin Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban tawagar gyaran fanshon ma’aikata (PRTT) da gwamnati ta rushe.

A hukuncin da alkalin kotun, Okong Abang, ya zartar ranar Laraba, ya bayar da umarnin a sake kamo Maina ”duk inda aka gan shi”.

Lauyan hukumar EFCC, Mohammed Abubakar, ya ce an bayar da belin Maina a kan kudi miliyan N500 da kuma mai tsaya masa; wanda dole ya kasance Sanata mai ci da zai ajiye miliyan N500 a kotu.

Lauyan ya rubuta takardar korafi zuwa kotun inda a ciki ya zargi Maina da saba sharuda da ka’idojin belin.

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci ta gurfanar da Maina a gaban kotu bisa tuhuma goma sha biyu da ta shirya a kansa da kuma wani kamfani mai suna ‘Common Input Properties & Investment Limited”.

Bayan bawa hukumomin tsaro izinin kama shi, kotun ta bawa EFCC damar gurfanar da shi tare da tuhumarsa a kebance.

Kazalika, kotun ta saka ranar 23 ga watan Nuwamba, domin bawa Sanata Ali Ndume, wanda ya tsayawa Maina, damar yin bayanin dalilin da zai hana shi rasa kudin beli N500m da ya bayar.
A cewar kotun, za’a saka kudin da Sanatan ya biya a aljihun gwamnatin tarayya saboda saba ka’ida da sharudan da aka bayar da Maina beli a kansu.

Kotun ta dauki wannan mataki bayan ta gamsu da hujjar EFCC a kan cewa Maina ya ki halartar zaman kotu har sau hudu a jere ba tare da wani dalili mai kwari ba.

Kafin Sanata Ndume ya karbi belinsa, Maina ya shafe tsawon watanni bakwai a gidan yarin Kuje.

EFCC ta na zargin Maina da wawure kimanin biliyan biyu ta hanyar amfani da kamfanin ”Common Input Properties & Investment Limited”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here