Kotu ta Bayar da Umarnin Kamo Shugaban PDP, Turaki
Kotu ta bayar da umarnin kamo Kabiru Turaki saboda kin bayyana a gabanta kan tuhumar bayar da bayanan karya ga yan sanda.
Rundunar yan sanda na tuhumar shugaban jam’iyyar na PDP da laifin yaudarar hukuma a wata takardar koke da ya shigar a 2022.
A zaman shari’ar na yau, Mai Shari’a U.P. Kekemeke, ya ce Turaki ba shi da wani gamsasshen dalili na ƙin amsa sammacin kotu.
Abuja – Wata babbar kotu dake Abuja ta bayar da umarnin kamo Kabiru Tanimu Turaki, shugaban wani tsagi na jam’iyyar PDP a matakin kasa.
Kotu ta bayar da umarnin cafko shugaban jam’iyyar ne bayan ya gaza bayyana a gaban kotun a ranar Alhamis, 26 ga Maris, 2026.
Kotu ta bada umarnin kamo shugaban PDP
Alƙalin kotun, Mai Shari’a U.P. Kekemeke, ya bayyana cewa tsohon ministan ba shi da wani dalili na ƙwarai da zai sa ya ƙi amsa sammacin kotu, in ji rahoton The Cable.
Read Also:
Rundunar ‘yan sandan Najeriya (IGP) ce ta shigar da ƙarar Turaki tana tuhumarsa da laifi guda ɗaya, wanda ya shafi zargin bayar da bayanan ƙarya ga hukumar ‘yan sanda a cikin wata takardar koke da ya rubuta tun a watan Oktobar shekarar 2022.
Wannan umarni na kama shugaban tsagin jam’iyyar ta PDP ya zo ne bayan da ya yi kunnen uwar shegu da zaman kotun na baya.
Neman sauya alkali a shari’ar shugaban PDP Tun a zaman kotu na ranar 28 ga watan Janairu, aka tsara za a gurfanar da tsohon ministan, amma rashin halartarsa ya sa aka ɗage zaman.
A lokacin, lauyan wanda ake kara ya bayyana cewa wanda yake karewa bai zo kotun ba ne saboda sun rubuta wasiƙa ga babban alƙalin babbar kotun Abuja suna neman a canja alƙalin da ke sauraron shari’ar zuwa wani daban.
Jaridar The Nation ta ruwaito lauyan Turaki ya bayyana cewa sun shigar da koke ne saboda rashin amincewa da adalcin kotun ga wanda yake karewa wa.
Sai dai, Mai Shari’a K.N. Ogbonnaya, wanda ya taɓa zama a kan shari’ar, ya bayyana cewa:
“Shigar da koke ga babban alƙali ba zai iya dakatar da ci gaba da shari’ar manyan laifuffuka ba, sai dai idan umarni ya fito daga ofishin babban alƙalin.”















