Kotu ta yi Watsi da ƙarar NBC kan Cin Tarar Gidajen Radiyo da Talbijin a Najeriya

 

Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da hukumar kula da gidajen radiyo ta Najeriya NBC ta shigar gabanta, tana neman kotun ta rusa hukuncin da babbar kotun tarayya ta yi na hana ta cin tarar wasu gidajen radiyo da talbijin a faɗin ƙasar.

Yayin da yake gabatar da hukuncin, babban kotun Mai shari’a Oyebiola Oyewumi a madadin alkalan kotun uku ta amince da hukuncin babbar kotun tarayya, wanda ya hana hukumar NBC cin tarar gidajen labari 45 a ranar 1 ga watan Maris na 2019 saboda zarginsu da saɓa ƙa’idar dokar yaɗa labarai ta Najeriya.

Kotun ɗaukaka ƙarar ta ce hukumar NBC ba ta hurumin cin tarar gidajen labarai a ƙasar.

Mai Shari’a Oyewumi ta ci gaba da cewa a ƙarƙashin dokokin Najeriya ana cin tara ne ga waɗanda aka samu da laifin saɓa doka, kuma kotu ce kawai ke da hurumin yin hakan, ba mutumin da aka yi wa laifi ba.

Tun da farko babbar kotun tarayyar ta ce matakin na NBC ya saɓa wa dokokin Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here