Daliban Jami’ar Greenfield: Masu Garkuwar Sun Nemi Kudin Fansa N800m

 

Masu garkuwa da suka sace dalibai a Jami’ar Greenfield a Kaduna sun nemi kudin fansa.

Yar uwan daya daga cikin daliban ta ce masu garkuwar sun ce a biya su Naira miliyan 800.

A cewarta, sun fara azabtar da daliban sun kuma ce za su halaka su duka idan ba a biya kudin fansar ba.

Daya daga cikin iyalan daliban Jami’ar Greenfield da ke Kaduna ya ce yan bindigan sun bukaci a biya Naira miliyan 800 matsayin kudin fansa kafin su sako daliban 23, Vanguard ta ruwaito.

“Ana tattaunawa, masu garkuwar sun tuntubi wasu iyalan daliban suna neman a biya Naira miliyan 800,” a cewar, Georgina Stephen, yar uwan daya daga cikin daliban da aka ace.

Ta ce masu garkuwa da mutanen sun bukaci yan gidansu su biya Naira miliyan 8 kudin fansa kafin su sako yar uwanta da ke tsare a hannunsu.

A cewar Georgina, daliban 23 da aka sace sun kunshi mata 14 da kuma maza 6 da kuma ma’aikatan jami’ar.

Ta ce masu garkuwa da mutanen suna azabtar da daliban inda suka ce idan ba a biyan kudin ba, za su halaka dukkan daliban da suka sace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here