2023: Kudirin Gwamnan Kogi ya Fara Bayyana Kan Zama Shugaban Kasa
Ana sanya ran tseren neman zaben Shugaban kasa na 2023 zai kankama a shekarar nan ta 2021.
Ana kuma sanya ran cewa mafi akasarin masu neman takara za su bayyana kudirinsu a sabuwar shekarar.
Suna daya da ke ta tashi a tseren shine na Alhaji Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi.
Fastocin kamfen din gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya billo a wasu manyan hanyoyi a jihar Kano, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
An gano fastocin da ke dauke da rubutun da ke nuna kudirin gwamnan na neman shugabancin kasa a 2023, a wasu yankunan cibiyar kasuwancin na arewa.
Read Also:
A cewar rahoton, fastocin basa dauke da logon kowacce jam’iyya amma akwai babban rubutu da ke cewa “Don samun chanji 2023, ku zabi Yahaya Bello a matsayin Shugaban kasa, Jumhuriyar Najeriya.”
An manna fastocin a wasu muhimman wurare a jihar, ciki harda Murtaa Muhammad Way, hanyar filin jirgin sama da kuma hanyar Sani Marshal.
Sauran yankunan da aka gano fastocin sun hada da hanyar Race Course, hanyar Bompai da wasu yankuna na unguwannin gidan gwamnatin Kano.
Wasu yan Najeriya a shafin Twitter sun yi sharhi a kan fastocin.
Akibu Oluwaleke Waliu ya rubuta:
“Ko kamshin tikitin hawa kujerar Shugaban kasar Najeriya ba za ka ji ba a 2023.”
Ma’aji Umar ya rubuta:
“Wannan mutumin na so ya wofantar da kudin Kogi, wani ya fada masa idan lokaci ya kure.”
Ralph Eboigie ya rubuta:
“Ko zaben fidda gwani ba zai ci ba. Gwamnan da ya kasa. Babu wani abun rubutawa game da shugabancinsa a Kogi.”