Kungiyar MURIC ta yi Kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Kula da Tubabbun ‘Yan Boko Haram/ISWAP

 

Kungiyar kare hakkin musulmai (MURIC) tayi kira ga gwamnatin tarayya da hukumar sojojin Najeriya akan shiryawa da tubabbun ‘yan Boko Haram da mayakan ISWAP.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata takarda wacce ta saki a ranar Alhamis inda tace ya kamata a kyautata musu tamkar ‘yan uwan da suka bata aka tsincesu yanzu.

MURIC ta bukaci a koya musu sana’o’i don su samu sababbin hanyoyin da za su cigaba da kulawa da iyalansu da kawunansu nan gaba.

Kungiyar kare hakkin musulmai ta MURIC tayi kira ga gwamnatin tarayya da hukumar sojojin Najeriya akan shiryawa da tubabbun mayakan Boko Haram da ISWAP.

Newswire ta ruwaito cewa, MURIC ta bayar da wannan shawarar ne a wata takarda da ta saki a ranar Alhamis inda tace ya kamata a kula da tubabbun ‘yan ta’addan tamkar ‘yan uwa wadanda suka bata aka gansu.

A koyar da tubabbun ‘yan ta’adda sana’o’i

Ta bayar da shawarar ne inda tace ya kamata a koyar da su sana’o’i don su samu damar cigaba da kulawa da kawunansu da iyalansu nan gaba.

Ta hori mutane da su guji tsangwamarsu

MURIC tace nasarar yaki a zuciyar mazaje take don haka shiryawa da tubabbun ‘yan ta’addan ne kadai hanyar da za a samu nasarar cin yakin da gaske.

Yankin arewa maso gabas a Najeriya sun fuskanci wani sauyin yanayi na tubar mayakan Boko Haram da ISWAP, wanda dubbaninsu suka zubar da makamansu.

Sai kuma yankin suka samu karuwar jama’a wadanda su ne tubabbun ‘yan ta’addan. Wannan sabon nauyi ne da ya hau kan gwamnatin jahar.

Gwamnan jahar, Farfesa Babagana Umara Zulum, jiya ya roki gwamnatin tarayya da hukumar sojin Najeriya a kan su taimaki jaharsa wurin shiryawa da tubabbun mayakan.

MURIC tana taya hazikin Gwamna Zulum rokon FG da sojojin Najeriya da su yi iyakar kokarinsu wurin taimakawa gwamnatin jahar ta shirya dasu. Ya dace a taya gwamnan da kullum yake cikin sojoji a filin daga dare da rana yana shiga asibitoci da azuzuwa don tabbatar da ayyukan jahar suna tafiya yadda ya dace.

Mu na so mu tunatar da cewa neman shiri ya fi yaki sauki kuma ya fi kawo cigaba da zaman lafiya.

Don haka FG ta tsaya tsayin daka wurin ganin an saukaka komai. Ya kamata a zaunar da tubabbun mayakan Boko Haram da na ISWAP a koya musu sana’ar da za su amfani rayuwarsu da ta iyalansu nan gaba.

MURIC ta bukaci jama’a kada su tsangwamesu, su nuna musu soyayya. Kada su kuskura su kyamacesu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here