Akalla Akwai Kungiyoyi sama da 30 da ke Fafutukar Ballewa Daga Najeriya – Sanata Abaribe
Santa daga yankin kudu maso gabas ya bayyana goyon bayansa ga kungiyar ta’addanci ta IPOB .
Sanatan ya ce, akalla akwai kungiyoyi sama da 30 da ke fafutukar ballewa daga Najeriya a yankin.
Ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa a wata hira a gidan talabijin na Channels jiya Talata.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, Enyinnaya Abaribe, ya ce akwai sama da kungiyoyin ‘yan aware 30 a yankin Kudu maso Gabas da ke da zimmar aiwatar da burinsu na kafa Biafra.
Abaribe, a wata hira da aka yi da shi a ranar Talatar da ta gabata a gidan Talabijin na Channels, ya yi zargin cewa ana kuntatawa mutanen yankin kuma ana yi musu rashin adalci.
Legit.ng Hausa ta rahoto daga Daily Trust inda Abaribe ke cewa:
Read Also:
“Babbar matsalar da kafafen watsa labarai ma ke da ita ita ce danganta komai da ya faru da kungiyar IPOB yankin Kudu maso Gabas.
“Ba za ku yi imani cewa akwai kungiyoyi daban-daban na ‘yan aware sama da 30 ba. IPOB, MASSOB, suna da yawa kuma kowanne daga cikinsu yana tafiya akan abu guda ne.
“Dalilin da yasa muke tayar da zaune tsaye a ko’ina a cikin kasar shine cewa wasu mutane basa iya gane bambancin mu.”
Ya ce gwamnatin yanzu za ta iya murkushe kungiyoyin ‘yan aware a shiyyar, amma ba za ta iya kashe akidar ba idan ba a magance musabbabin tashin hankalin ba.
Ina goyon bayan mutane, ciki har da IPOB, inji Abaribe Da aka tambaye shi ko shi mai goyon bayan IPOB ne, Abaribe ya ce:
“Ni mai goyon bayan koken mutanenmu ne kan rashin adalci … ina tare da mutanena.” Ya ce bai yi nadamar tsayawa a matsayi daya daga cikin wadanda za su tsaya wa jagoran IPOB, Nnamdi Kanu a shekarar 2017 ba.